Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya ce babu wata barazana ko wasu maganganun bayan fage da za a yi masa kan zargin azurta kansa ta haramtacciyar hanya a lokacin da yake mulki, yana mai cewa babu ko da taku ɗaya da ya mallaka a kasashen ketare.

Shugaba Buhari ya shaida hakan ne a wani taron liyyafa da aka shirya masa a birnin Damaturu na Yobe inda yake ziyara.
Sannan shugaban ya ce yana alfahari ganin cewa ya yaki Boko Haram kuma ya ga karshensu abin da yake cewa ya dawo da ayyuka da harkoki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce ya sauke nauyi da alkauran da ya dauwakarwa ‘yan Najeriya lokacin rantsuwar kama aiki a 2015 na kawar da Boko Haram damar da daidaito a kasar.

Shugaban ya kuma shaida cewa hadin-kai da ya samu daga kasashe makwabtan Najeriya na daga cikin abubuwan da suka taimaka masa wajen yaki da ta’addanci.