Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin sahalewa dukkanin yan takara na jam’iyyu daban daban kan su yi amfani da filin wasa na Sani Abacha don gudanar da tarurrukan yakin neman zabensu.

Bayanin hakan ya fito ne daga hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba a jiya Litinin.

Kwamishinan ya ce bada wannan dama na daga cikin irin kudirin gwamnatin ta Kano wajen ganin kowace jam’iyya an bata cikakkiyar damar gudanar da ayyukan ta a fadin jihar.

Muhammad Garba wanda shi ne mai magana da yawun babban kwamitin yakin neman zaben gwamna da mataimakinsa a jihar Kano karkashin jam’iyyar APC, ya ce kowace jam’iyya na da damar yin taro a filin wasan na Sani Abacha, tare da amfani da dukkan kayan aikin da ke cikin filin wasan, matuƙar ta cika ka’idar hakan daga hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa, gwamnatin Kano za ta cigaba da bada dukkan damar da ta dace bai daya a tsakanin jam’iyyu domin girmama harkokin dimokuraɗiyya.

Daganan sai kwamishinan ya bayyana fatansa da kiransa ga jam’iyyun siyasa a jihar kan a yi tarurrukan yakin neman zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: