Gwamnatin Tarayya ta ba wa manoma 210 da ambaliya ta shafa a Jihar Kaduna tallafin irin shuka don rage musu radadin da suka shiga.

Mataimakiyar Darakta a Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya, Misis Omotosho Agbani, ce ta raba tallafin, wanda ta ce wani shiri ne na taimakon manoman da ambaliya ta shafa a 2022 da sabbin kayan aikin noma.
Ta ce, suna son manoma su yi amfani da wannan tallafi don habaka nomansu.

A cewarta, tallafin wani shiri ne na taimakon manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a 2022 da sabbin kayan aikin noma.

A cewarta, kayayyakin sun hada da irin tumatir, albasa, kayan lambu, ’ya’yan itatuwa da sauransu.
Ta ce, ambaliyar ruwa ta a 2022 ta haifar da damuwa ga manoma tare da raba mutum miliyan 1.4 da muhallansu a fadin Najeriya.
Ta kara da cewa, baya ga mace-mace da asarar gidaje da ababen more rayuwa da aka samu, ambaliyar ta shafi gonaki 332,327.