Hukumar kashe gobara ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa wata gobara ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane hudu a garin Zariya da ke Jihar.

Mai magana da yawun hukumar na garin Zariya Muhammad Umar ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.
Kwamandan ya ce mutanen da su ka raya rayukan su wani Limami ne mai suna Muhammad Sani da matar Raulatu da kuma ‘ya’yansu Fatima Sani da Hashim Sani.

Muhammad Umar ya kara da cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na dare a layin Hajiya Mai Tuwo Low Cost da ke karamar hukumar Zariya ta Jihar.

Umar ya bayyana cewa bayan gobarar ta cinye adadi mai yawa na gidan aka kira hukumar.
Shugabana ya ce bayan zuwan jami’an su gurin sun samu nasarar kashe wutar.
Umar ya ce daga bisani an kaima matata garin Dogarawa a sabon gari domin yi musu sutura