Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya jinjinawa shugaban kasa Muhammad Buhari bisa kokarin da ya yayi wajen yaki da mayakan boko haram da ‘yan bindiga da su ka addabi fadin Najeriya.

Wike ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin Jihar da ke garin Fatakwal a ranar Lahadi bayan kammala jera furanni a gurin bikin ranar tunawa da ‘yan mazan jiya.
Nyesom Wike ya kara da cewa jami’an soji na yakar mayakan boko haram da ‘yan ta’adda a Jihohin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma harma da ‘yan bindiga a Jihohin kudu maso gabas.

Wike ya ce shugaban na aikin dawo da zaman lafiya a Jihohin da ke fama da rikice-rikincen ‘yan ta’adda.

Gwamna Wike ya bayyana cewa samar da zaman lafiya da shirya sahihin zabe su ne jiga-jigan abubuwan da za a ci gaba da tunawa da shugaba Buhari ko bayan ya bar mulki.
Daga bisani Wike yayi addu’a ga shugaba Buhari da sauran shugabanni domin sauke nauyin da su ka dauka.