Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan bankin Najeriya da wasu wakilai daga bankin bunƙasa tattalin arziƙin Larabawa a Abuja.

Shugaban ya gana da mutanen a yau a fadarsa da ke Abuja bayan raɗe-raɗin yunƙurin kama gwamnan bankin a ranar Lahadi.

Rahotannin sun nuna cewa jami’an hukumar DSS sun mamaye ofishin gwamna  bankin bayan dawowarsa daga daga ƙasar waje.

Sai dai wata kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta dagakar da hukumar ƴan sandan farin kaya daga kama gwamnan bankin.

Yunƙurin kama gwamnan ya boyi bayan ƙin halartar gayyatar da majalisar wakilai ta yi masa a ƙarshen shekarar da ta gabata.

Gwamnan bankin ya halarci ganawarsa da shugaban ƙasa bayan karɓar baƙin larabawa a yau.

Zaman ya samu halartar shuagaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya da ministan harkokin kasashen  waje gwamnan jihar Borno har ma da jakadan Najeriya a ƙasar Sudan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: