Babban bankin Najeriya CBN ya ce a halin da ake ciki ya na roƙon bankin ƴan kasuwa don ganin sun karɓi isassun sabbin kuɗaɗen da za su wadata jama’a.

Ƙasa da makonni biyu su ka rage don ganin an daina karɓar stofaffin kuɗi na naira 200, 500 da naira 1000 a Najeriya.
Sai dai bankin CBN ya baiwa bankin ƴan kasuwa umarni don ganin an cika injin cirar kuɗi da sabbin kuɗaɗe yadda za a sauƙaƙa lamarin ga jama’a.

Shugaban sashen shari’a na bankin Najeriya CBN Salam-Alada ne ya bayyana haka a wajen wani taron wayar da kai da ya gudana a jihar Lregas.

Ya ce a halin da ake ciki bankunan ƴan kasuwa na cigaba da karɓar sabbin kuɗaɗe daga hannun CBN don ganin dokar da bankin ya saka ta yi aiki yadda ya kamata.
Kwanaki 12 ne su ka rage gwamnatin ta haramta karɓar tsofaffin kuɗaɗe daga hannun mutane wanda ta saka wasu sharruɗa.
Kwanakin da wasu miutane ke kallon hakan a matsayin barazana duba ga cewa har yanzu ba a kai ga wadata jama’a da sabbin kuɗin a hannunsu ba.
Sai dai bankin ya ce za su cigba da bibiyar injinan cvirar kuɗi na ATM domin tabbatar da cewar bankuna sun saka sabbin kuɗaɗe a ciki.