Shugaban hukumar yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA Janar Buba Marwa ya tabbatar da cewa hukumar su tasha kama sanannun ‘yan siyasa masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Buba Marwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tabbatar da shirin majalisar dokokin Najeriya yarjewa da dokar fara gudanar da gwajin miyagun kwayoyi akan ‘yan siyasa kafin tsayawar su takara ko rike wani mukami a office.
A yayin wata ganawa da Buba Marwa yayi da BBC ya ce su na kokarin dabbaka hakan ne domin ba tun yanzu ba su ke kama ‘yan siyasa da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Marwa ya ce hakan bai riga da ya zama doka ba amma nan gaba za a tabbatar da dokar.

Shugaban ya kara da cewa kawo yanzu kwamitin Majalisar Dokokin ya mika shawarar amincewa da hakan a hukumance.