Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da ceto dalibai biyu daga cikin daliban shida na makarantar firemari ta LEA wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a Alwaza karamar hukumar Doma ta Jihar a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Rahman Nansel ya tabbatar da hakan a yau Asabar ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Rahman ya ce jami’an sun samu nasarar ne da misalin karfe 2:30 na rana a kauyen Sabon Kwara da ke Jenkwe a karamar hukumar Obi a Jihar.

Nansel ya kara da cewa hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ne su ka kubtar da daliban a yayin wani sintrin neman daliban da jami’an su ka gudanar.

Kakakin ya ce bayan kubtar da daliban biyu jami’an sun sake dukufa domin su ceto ragowar yaran hudun da ke hannun masu garkuwar.

Nansel ya kara da cewa bayan ceto daliban an mika su ga Asibiti domin duba lafiyar su daga bisani a mika su ga iyayen su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: