Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da barkewar cutar Diphtheria, a kananan hukumomi 13 da ke fadin jihar.

Kwamishinan lafiya Na Jihar Aminu Tsanyawa ne ya bayyana hakan, jiya Asabar yayin bayani akan Barkewar cutar Lassa da kuma Diphtheria din a jihar.
Yace an samu rahoto akan kamuwar kimanin mutane 100, inda a cikinsu tuni mutane 3 sun rasa rayukansu.

Yace Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hadar da Ungogo, Nasarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kiru, Rano da kuma Gwarzo.

Ya kuma fadar cewa a cikin mutane 100 da ake zargin sun kamu, mutane 8 an tabbatar da kamuwarsu. Yayin da ake dakon sakamakon ragowar.
Ya kuma bayyana cewa, mutane 27 an kwantar dasu a Asibiti ana basu magani, yayin da mutum 41 kuma tuni an sallamesu.
Ya kuma bayyana cewa ranar 10 ga watan Janairun nan, sun karbi rahoton cutar Zazzabin Lasa daga Asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase dake Kano.
Sannan yace an baza jami’ai Dan yin bincike a kai, an dauki samfuri zuwa dakin gwaje-gwaje. Bayan kwanaki uku an tabbatar akwai cutar ta Zazzabin Lassa.