Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin tutar jamiyyar Labour Party, Peter Obi, ya ce shi da abokin takararsa, Yusuf Datti ba su da wani tabo na cin hanci da rashawa.

Kuma ya ce ba su taba satar kudin gwamnati ba, don haka su ne su ka fi cancanta a zabe su a kakar babban zabe na watan Fabrairu mai zuwa.

Ya bayyana haka ne a jiya Jum’a a filin wasa na Rwang Pam da ke babban birnin Jos na jihar Plateau yayin da yake yakin neman zabe.

Peter Obi ya kara da cewa duk wanda za a ji yana tuhumarsa akan koma menene sai dai ta wata siffar amma ba akan cin hanci da rashawa ba.

Har ila yau ya ce duk wasu alamuran more rayuwa na kasar zai kula da su tare da adana su don ganin an yi amfani da su ga alummar da ta dace.

Dan takarar ya cigaba da cewa shi da mataimakinsa da kuma jamiyyarsu ta Labour Party, matasa ne masu jini- a-jika da kuma kaifin basira ba kamar yan takarkarun sauran jam’iyun ba da suke dattijai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: