Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya ce zai aiwatar da aiki na Naira Tiriliyan 1.9 na gyaran tituna 44 bayan da ya yi gagarumin aikin gyaran tituna 21 na Naira biliyan 621 a karkashin tsarin biyan haraji.

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana haka a ranar Talata a taron shekara-shekara na kungiyar masu motocin haya ta kasa NARTO karo na 23 a Abuja.

Ya ce, NNPC ta tallafa wa gwamnatin tarayya wajen gyara tituna kuma a matakin farko na sama da kilomita 1,800 da darajarsu ta kai Naira biliyan 621, sun samu ci gaba mai kyau a kan hakan.

Shugaban na NNPC ya ce kashi na 2 na tiriliyan 1.9 Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da shi a makon da ya gabata don rufe hanyoyi 44.

Kamfanin ya bayyana aan a matsayin gagarmar nasara da za su yi alfahari da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: