Gwamnan jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ya umarci wasu ma’aikatun jiharsa masu alaka da kudi da su gaggauta bude sabbin shiyyoyi na bankin Borno Renaissance Mircrofinance a dukkan kananan hukumomin jihar.

 

Wannan umarni dai ya shafi ma’aikatun kudi, ilimi, kimiyya, fasaha da kirkira, sannan ana bukatar su bude bankunan da cibiyoyin ICT a kananan hukumomi 27 na jihar.

 

Umarnin na Zulum na zuwa ne yayin da wa’adin CBN na daina amfani da tsoffin kudi ke karatowa sannan ya gano kananan hukumomi 25 daga 27 na jiharsa basu da bankuna.

 

Rashin bankuna a yankunan Borno ya samo asali ne daga rikicin Boko Haram na tsawon shekaru 12 da ya dabaibaye yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

 

Zulum ya ba da umarnin ne a ranar Laraba 25 ga watan Janairu a birnin Maiduguri yayin wata zama da masu ruwa da tsaki na jihar, ciki har da Shehun Borno, wanda ya samu wakilcin Wazirin Borno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: