Mahaifin ƴan biyun mai suna Muhamamad Adam ya wallafa a shafinsa na facebook cewar sakacin ma’aikatan asibitin ya sa su ka hana kowa shiga su sai matar kuma ya ke zargin sun barta ta gudu bayan ganota.

A ranar Juma’a aka haifi tagwayen kuma mahaifinsu wanda Ɗan’jarida ne ya wallafa cewar ya rabauta da samunsu.

Sai dai a yau Lahadi ya wallafa cewar wata mata da ake zagi mai satar jarirai ce ta kutsa kai ɗakin masu jinya yayin da aka hana kowa shiga tare da yunƙurin sace guda daga ciki.

Mahaifin tagwayen ya yi zargin sakacin ma’aikatan asibtin, da ya janyo har aka bar matar ta shiga ba tare da an bar ko ma’aikatan jinya sun shiga ba.

Muhammad Adam wanda aka fi sani da Yaya Muhammad, ya ce ko masu kula da shige da ficen asibitin ba su yi nasarar kama matar ba har sai da ta tsira duk da yunƙurin da ta yi na satar guda cikin ƴaƴansa.

Hukumomin asibitin ba su ce komai a dangane da lamarin ba, amma ko a kwanakin baya sai da aka zargi sakacin wani likita a wani asibiti a Kano da sanadin ruɓewar hanun wani jariri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: