Gwamnonin jam’iyyar APC sun bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanya baki domin a ci gaba da karbar tsofaffin kudade da sabbin a kasar.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa’i ya bayyana hakan bayan wata ganawar sirri da su ka yi da shugaban a fadar sa da ke Abuja a ranar Juma’a.
El’Rufa’i ya ce bayan da babban bankin kasa na CBN ya karbi sama da Naira Tiriliyan biyu na tsofaffin kudade,amma naira biliyan 300 kadai ya buga na sabbin kudin wanda hakan ba zai wadatar da Al’ummar kasar ba.

A yayin ganawar ciki harda gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi kira ga bankin na CBN da ya buga akalla rabin abinda aka tara.

Ganduje da gwamnonin jam’iyyar sun bayyana wa shugaba Buhari irin wahalar da talakawan kasar ke sha tare da asarar kayayyakin da ‘yan kasuwa ke yi sakamakon rashin wadanda basa siyan kayan.
Daga bisani kuma ya bayar da misali yadda masu sana’ar sayar da tumatur su ka tafi Jihar Legas da shi amma ya lalace sakamakon rashin kudin da mutane ba su dashi da za su saya.
Gwamna El’Rufa’i ya ce tawagar gwamnonin sun roki shugaba Buhari da ya sake yin nazari akan halin da mutanen kasar ke ciki.
El’Rufa’i ya kara da cewa shugaban gamayyar gwamnonin Atiku Bagudu ya sake wata ganawa da shugaban shi kadai ba domin sake janyo hankalin shugaban wajen ganin an janye dokar daina amfani da tsofaffin kudade.
A yayin jawabin gwamna Ganduje ya ce shugaba Buhari yayi alkawarin yin duba akan bukatar da su ka gabatar masa.