Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina sun hallaka mutane 41 a wani sabon  hari da su ka kai.

Maharani sun hallaka mutane 41 daga cikin ƴan banga yayin das u ka yi musu kwanton ɓauna.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Isah Gambo ya bayyana a wata sanarwa day a aikewa Matashiya TV ranar Juma’a.

Ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis yayin da ƴan bndigan su ka kai wani hari ƙauyuka kusan 11 a jihar Katsina.

Sanarwar ta ce a ranar Laraba ƴan bindiga sun kai hari Unguwar Audu Gare a Kandarawa da ke ƙaramar hukumar Bakori kuma su ka sace shanu 50 da awaki 30.

Sai dai ƴan sa kai sun bi sawun ɓarayin har zuwa dajin Yargoje kuma a nan ne aka yi musu kwantoin ɓauna aka hallaka 41.

Tuni jami’an su ka kwaso gawarwakin mutanemn da aka kasha tare da haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin kamo waɗanda su ka aikata hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: