Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Nassarawa domin buɗe wasu manyan ayyuka da gwamnatinsa ta aiwatar
Shugaba Buhar ya sauka a Lafiya babban birnin jihar.

Daga cikin ayyukan da gwamnatin ta aiwatar har da makarantar samar da kayan aikin gona na zamani wanda aka samar domin samawa matasa aikin yi.

Mataimakin shugaban makarantar Farfesa Muhammed Haruna ya tabbatar da cewar makarantar za ta samawa matasa aikin yi kuma za ta kawo ƙarshen ƙarancin abinci da ake fama da shi a Najeriya.

Ya ƙara da cewa za a ƙaddamar da makamanciyar makarantar a nan gaba
Shugaban zai koma Abuja bayan kammala ƙaddamar da ayyukan da kuma halartar taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na jam’iyyar APC  a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: