Aƙalla shaguna gomna wata gomara ta cinye a wata kasuwa a jihar Yobe.

Lamarin ya faru a sanadin wutar lantarki kamar yadda shaidu su ka tabbatar.
Gobarar ta tashi a yankin Sabon Fegi kusa da gidan tsohon gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam.

Wani mai suna Ahmed Idris Ahmed ya shaida cewar shaguna goma ne su ka ƙone kuma gobarar ta faru ne sanadin wutar lantarki da ta haddasa.

Mafi akasarin shagunan das u ka ƙone ana siyar da takalma da kayan sakawa da kayan amfanin yau da kullum.
Ana zargin gobarar ta cinye dukiyar miliyoyin kuɗaɗe.
Har lokacin da mu ke kammala wannan labara hukumar kasha gobara a jihar ba ta ce komai a dangane da lamarin ba.