Aƙalla mutane tara ne su ka rasa rayukansu yayin da wasu masu iƙirarin jihar su ka kai hari sansanin ƴan gudun hijira a jamhuriyar Nijar
Masu iƙirarin jihadin sun kai harin ne a ranar Laraba a sansanin Tahoua yankin da ke iyaka da ƙasar Mali.

Mutane tara aahallaka yayin da guda ya ji rauni kuma har yanzu ba a ga mutane shida daga ciki ba.

Wani daga cikin jami’an tsaro ya tabbatar da kai harin sai dai ba yi wani ƙarin bayani a kai ba.
An ci gaba da kai hare-hare yankin Tahoua tun bayan da aka samar da sansanin ƴan gudun hijira da ke zaune daga ƙasashen urina Faso, da Mali da kuma wasu daga jamhuriyar Nijar.

KO A WATAN Maris ɗin shekarar 2021 sai da aka hallaka mutane 141 fararen hula yayin da aka hallaka sojojin ƙasar Nijar 14 a watan Mayu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: