Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya yi barazanar ƙwace lasisin filayen duk bankin da ya yi nuƙusani wajen biyan sabbin kuɗi ga kwastomominsa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin day a ziyarci wasu bankuna a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Gwamnan ya yi zargi wasu bankuna da haddasa dalilin ƙarancin sabbin kuɗi da aka sauyawa fasali a hannun jama’a.

Zulum ya nuna damuwarsa a kan yadda ɗruruwan mutane ke tsaye sun a bin layi a injinan cirar kuɗi na ATM wajen cirar kuɗi.

Ya ce babu masu kuɗi a kan layi illa talakawa, kuma a tambayoyi daga garesu sun tabbatar masa da cewar wasu sun a kan layin cirar kuɗin tun ƙarfe uku na dare.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta yi albashi, kuma sun fitar da kuɗi domin jama’a babu wani dalili da zai sa mutane su kasa samun kuɗaɗensu cikin sauƙi.
A jawabinsa y ace gwamnatinsa bat a da matsala da matakin baban bankin Najeriya CBN domin dokar ba za ta jawo dogayen layin da ake fama da shi ba.