Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta kama manajan ayyuka na wani bankin ‘yan kasuwa kan boye sabbin takardun naira a Abuja.

 

Manajan ayyukan babban bankin ‘yan kasuwa da ke kwaryar birnin Abuja a yau, 6 ga Fabrairun 2023, ya shiga hannun jami’an EFCC kan kin zuba kudi a ATM din bankin duk da Naira miliyan 29 da aka samu na sabbin kudin a ma’adanar kudin bankin.

 

Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, kafin a yi awon gaba da shi don tuhuma, jami’an sun umarci a zuba kudin a ATM kuma a fara biya ta kanta domin rage radadi ga kwastomomin da suka kwashe awoyi a layi.

 

Wannan bankadowar ya bayyana zagon kasa ga dokokin kudi na gwamnati wanda wasu bankunan ke yi.

 

Hukumar EFCC za ta cigaba da zagaye tare da sa ido da kuma kai ziyarar ba-zata bankuna a fadin kasar nan domin duba ma’adanar kudinsu tare da tantancewa ko da gangan suke kin zuba sabbin kudin.

 

Sama da rassa biyar na bankuna a yau jami’an EFCC suka mamaye a Abuja. An yi irin hakan a wasu sassan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: