Rahotanni daga jihar Borno na nuni da cewar wata gobara ta ƙone sansanin ƴan gudun hijira a Maiduguri ta jihar Borno.

Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 11:00am na safiyar yau Litinin.

Kayan abinci masu yawa ne su ka ƙone yayin da gidaje da sauran kayan amfani su ka ƙone ƙurmus.

Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida cewar gobarar ta yi mummunan ta’adi.

Gobarar wadda ta tashi a sansanin ƴan gudun Hijira na Muna Garaje ba a gano sanadin faruwarta ba.

Sai dai babu rahoton rasa rai a sanadin gobarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: