Hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta gano wasu makudan kudade Naira miliyan 258 a wani dakin ajiya na bakin Najeriya yayin da ake fama da karancin sabbin Naira.

Azuka Oguga, mai magana da yawun hukumar ce ta bayyana hakan, inda ta ce an gano kudaden ne a wani dakin ajiyar kudi na hedkwatar bankin Sterling da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jami’an ICPC sun gano kudade Naira miliyan dari biyu da hamsin da takwas (N258m) a makare a ma’ajiyar hedkwatar bankin Sterling da ke Abuja.

A cewarta, bincike ya nuna cewa, babban bankin Najeriya (CBN) ya ba Sterling kudaden domin rabawa ‘yan Najeriya, amma bankin ya gaza yin hakan.

A bangare guda, ya hukumar ta kama manajan bankin Keystone da ke Mararaba a jihar Nasarawa bisa laifin kuntatawa kwastomomi game da sabbin Naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: