Helikwatar tsaro ta ƙasa a Najeriya ta tabbatar da kashe ƴan ta’adda 77 tare da kama wasu 41 yayin da 340 su ka miƙa wuya.

Wannan ƙididdiga dai ta fito ne bayan tattara aƙaluma na ayyukan hukumar tsawon makonni biyu.
Daraktar yaɗa labarai na hukumar Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka yau yayin bayyanaayyukan hukumar ta saba yi lokaci zuwa lokaci.

Ya ce nasarar dasu ka samu na kamawa da kashewa da kuma masu miƙawuyan sun fito ne daga yankin arewa maso gabas, da arewa ta tsakiya da kuma yankin arewa maso yamma.

Sannan jami’an sojin sun ƙwato makamai ciki har da bindigu da harsashi mai yawa dasauran makamai da kuɗi ama da naira 77,000.
Sannan akwai wayoyin hannu da aka kama da kuma shanu da tumaki da aka ƙwato daga hannunƴan ta’addan.
Sannan jami’an sojin sun ƙwato makamai ciki har da bindigu da harsashi mai yawa dasauran makamai da kuɗi ama da naira 77,000.
Sannan akwai wayoyin hannu da aka kama da kuma shanu da tumaki da aka ƙwato daga hannunƴan ta’addan