Wasu matasa a Abuja sun gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da hukucin kotun ƙoli tare da zargin yin hukuncin domin farantawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

Daruruwan matasan sun yin zanga-zanga tare da zuwa helikwatar babban bankin Najeriya CBN da kuma ofishin ministan shari’a na ƙasa.

Mutanen sun buƙaci gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya CBN da kada su yi aiki da hukuncin da kotun ta yi.

A ranar Laraba matasan riƙe da alluna da kwalaye na nuna ƙin amincewa da hukuncin kotun ƙoli ta ƙasa har su ka zargeta da marawa ɗan siyasa baya.

Sannan sun gargaɗi ƴan Najeriya da kada su yi amfani da tsofaffin kuɗin da aka sauaywa fasali daga ranar 10 ga watan Fabrarirun da mu ke ciki.

Jigo daga masu zanga-zangar mai suna Obed Agu ya ce sun zargi kotunƙoli ta ƙasa da yin maƙarƙashiya wajen gudanar da sahihin zaɓe yayin da ta ƙi amincewa da abubuwan da za su inganta babban zaɓen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: