Shugaban hukumar ƙidaya ta Najeriya y ace aikin ƙidaya da za a yi a Najeriya za a yi har a dajin Sambisa.

Dajin Sambisa ya yi ƙaurin suna yadda mayaƙan Boko Haram su ka kafa sansani a cikinsa.

Shugaban hukumar Nasir Kwarra ne ya bayyana haka, ya ce duk da rashin tsaro da ake fuskanta a yankin za su tabbatar an yi ƙidayar mutanen da ke dajin.

Shugaban ya bayyana haka a Abuja yayin daya ke kaddamar da kwamitin yaɗa labarai na ƙidayar da ake shirin farawa.

Ya ƙara da cewa za su tabbatar an yiƙidayar dukkan mutanen da ke ƙasar da kuma gidajen da ke Najeriya.

Hukumar ta shirya aikin ƙidayar da za a fara kwanaki kaɗan bayan gudanar da babban zaɓen shekarar 2023 a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: