Wasu fusatattun matasa sun cinnawa bankunan keystone da Union wuta a jihar Ogun.

Wasu matasa dauke da kwalaye sun fito zanga zanga suna fama da karancin sabbin kuɗi.

A safiyar yau Litinin wasu matasa sun cinnawa bankunan Union da keystone sakamakon karancin kudin da suke fama da shi a cewar su.

A faifan bidiyon da aka wallafawa a shafin sada zumunta ya nuna yadda matasan suke kone kone a jihar Ogun.

Ko a makon da ya gabata a jihar Ogun matasan sun gudunar da zanga zanga a bisa karancin kudin.

A ranar juma ar makon da ya gabata shugaban kasa Mahammadu Buhari ya ce an daina karbar tsohohuwar naira 1000, da naira 500 tun a ranar 10 ga wata, sannan Kuma za a ci gaba karbar tsohohuwar 200 zuwa 10 ga watan Afrilu.

A wani bangaren Kuma likitoci sun ce ana ci gaba samun durkushewar harkar lafiya sakamakon karancin kudi da masu jinya suke fama da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: