Kasa Najeriya ta lashe gasar zane-zane ta duniya wadda aka gudanar a kasar Indiya.

Najeriya ta kasance kasar da ta zamo zakaran gwajin dafi a yayin da aka gudanar da gasar ta zane-zane wadda aka shafe makonni biyu ana gudanarwa a kasar ta Indiya.

 

Najeriya ta samu wakilci daga jihar Ekiti da Kuma Naija karkashin jagaracin kwamishinan harkokin zane-zane farfesa Ojo Bakare a yayin da aka gudanar da gasar.

 

Kasashe akalla 50 ne suka shiga gasar ta zane wadda kasar Najeriya ta lashe sai kuma ƙasar Uganda ta kasance mataki na biyu.

 

A yayin da yake maida martani farfesa Ojo Bakare ya ce ya kamata kasashe su maida hankali wajen habbaka harkar zane saboda mahimancinsa .

 

Sannan ya ci gaba da cewa harkar zane ba karamin abu bane a duniya Kamar yadda kasa Najeriya ta bada mamaki a yanzu.

 

Najeriya ita ce tilo wadda ta wakilci kasashen Afirka yayin gasar zane-zanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: