Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka dan takarar kujerar sanata tare da kone gawarsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa yakin neman zabe a jihar Enugu.

Mutuwar dan takarar na zuwa ne kwanaki biyu kafin gudanar da babban zabe a tarayyar Najeriya.
Bayan kashe Oyobi Chukwa yan bindigar sun kuma hallaka masu taimaka masa tare da cinna wa motarsu wuta kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar labour a jihar Chijioke Edeoga ya bayyana cewa jam’iyyun adawa ne ke kai masu hari ganin cewa zasu bada mamaki a babban zabe mai zuwa a ranar asabar 25 ga watan fabrairu.

Sai dai jam’iyyar ta Labor ba ta ce komai ba game da faruwar al’amarin, sai dai an rawaito dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Peter Obi na yin kira ga masu zabe da su gudanar da zabe lafiya da kwanciyar hankali.