Rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa za ta yi amfani da karfinta wajen dakile wanda duk za su kawo cikas ga zabe a Najeriya wanda zai gudana a ranar Asabar.

Babban daraktan wucin gadi mai kula da sashen yada labarai na rundunar Birgediya-Janar Tukur Gusau shine ya bayyana haka a yau Alhamis a yayin taron manema labarai da ya gudana helikwatar tsaro ta kasa dake birnin Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Kakakin hukumar tsaron ciki ta DSS Peter Afunanya, da Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi da kuma kakakin sojin saman Najeriya da sauransu.

A yayin wani taro da kwamitin tsaro ya gudanar tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shuwagabannin tsaron kasar sun bada tabbacinsu wajen tabbatar da gudanar da babban zaben kasar cikin lumana da kwanciyar hankali.

Kwamitin tsaron wanda ya hadar da babban hafsan hafso-shin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabo, da shuwagabannin rundunonin tsaro da babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba da Ministocin kasar da suka halarci zaman, sun shawarci Shugaba Buhari da ya mayar da hankalli game da kare rayukan al’umma a lokacin zabe da kuma bayansa.