Kungiyar masu sarrafa fulawa ta Nijeriya (FMAN) ta ce ta samar da cibiyoyin saye da sayarwa a jihohi 13, domin kawar da dukkan hatsin da ke tattare da noman wanda ya kunshi manoma 50,000 a shekara ta 2022-2023.

Manajan na shirin bunkasa alkama na FMAN Dakta Aliyu Sama’ila ne ya bayyana haka a lokacin bikin ranar noman alkama a karamar hukumar Bunza daje jihar ta Kebbi.

Ya ce aikinsu na daya shi ne samar da kasuwa ga manoman alkama a kasar nan.

Sun noma kadada 200 na alkama a shekarar 2022, kuma yanzu sun ninka shi zuwa 400 a bana a jihar Kebbi.

Haka kuma suna fadada sayayyarsu a matsayin masana’antu a duk fadin jihohin da ke noman alkama ta hanyar karin ma’aikatan tarawa da karfin ajiya.

Musamman, mun kafa cibiyoyin siyar da kayayyaki a fadin jihohin Arewa 13 don cire duk wani hatsin alkama daga manoma 50,000 a jahohin.

Jihohin su ne Kano da Kaduna da Jigawa da Kebbi da Sakkwato da Bauchi da Adamawa da Gombe da Filato da Taraba da Zamfara da kuma Yobe.

Kazalika don ci gaba da fadada noman alkama a kasar nan, dole ne mu kara yawan amfanin gonakin manoma, don sanya alkama ta yi gogayya da shinkafa da sauran noman rani.

Ya ce noman gonakin masu girman hekta 114 a fadin jihohin Arewa shida, domin ba da horo kan aikin noma na daga cikin shirinsu na ci gaba.

Jihohin sun hada da Adamawa da Borno da Gombe da Filato da Taraba da Yobe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: