Wasu yan daba dauke da bindigu sun kai hari rumfunan zabe a Oshodi da Itire a Legas, inda suka kona akwatunan zabe.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa maharan sun taho ne sanya da bakaken tufafi da face mask misalin karfe 11.30 na safiyar yau Asabar.

 

Wasu masu zabe da ba su iya tserewa ba a lokacin da yan daban suka iso sun jikkata.

 

Wasu majiyoyi sun ce yan ta’addan sun kai farkamin ne yan mintuna bayan jami’an tsaro da ke aikin zabe sun bar wuraren.

 

A cewar wani Tajudeen Haruna, bayan yan mintuna, yan daban sun bude wuta don tsorata masu zabe.

 

Hakazalika, wasu yan ta’adda sun kai hari a unguwar Itire, misalin karfe 12 na rana, suka tsorata mutane da masu zabe a yankin.

 

James Nwoke, ya yi ikirarin cewa an yi hakan da gangan ne don haka wasu mutane zabe.

 

Amma, akwai yan sanda da dama da sojoji a birnin Legas a yau Asabar don kiyayye rushewar doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: