Wasu fusatattun mutane sun yi kokarin kone ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da aka tsamu tasgaro tsakanin mabiya jam’iyyun siyasa a hedikwatar INEC da ke Takai da safiyar yau Lahadi 26 Faburairu, 2023.


A cewar sa an cinna wutar ne ta bayan ginin amma an kashe ta kafin ta yi barna mai yawa kuma jami’an tsaro sun watsa taron jama’a.
Sai dai, wasu mutane sun samu raunuka da kitimurmurar da aka fara da farko; amma an dauke su zuwa asibiti domin yi musu jinya yayin da aka kashe mutum hudu.
A fadin wani shaidan gani da ido na daban, lamarin ya barke ne a lokacin da aka fara tattara sakamakon zaben karamar hukumar.