Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa gobara ta tashi a babbar kasuwa ta ‘Monday Market’ da ke jihar Borno.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gobarar ta fara da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu kuma ta yadu zuwa bangarori daban-daban na kasuwar.

 

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a san musababbin abun da ya haddasa gobarar ba kuma jami’an kwana-kwana na nan suna kokarin kashe wutan.

 

Manema labarai sun rawaito cewa gobarar ta lakume daruruwan shaguna yayin da aka yi asarar dukiya na miliyoyin naira.

 

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Umaru Kirawa ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran NMajeriya, yana mai cewa sashin kwana-kwana na jihar da na tarayya daga bangarori daban-daban sun yi hadaka don dakile annobar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: