Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Kano na ci gaba da karɓar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a matakin ƙananan hukumomin.

Sai dai wakilin jam’iyyar NNPP ya koka dangane da rashin gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

Jam’iyyar NNPP ta yi zargin ɗan majalisar wakilai na yankin kuma ɗan takarar majalisar tarayya a jam’iyyar APC da tilasta han agudanar da zaɓe tare da saka baturen zaɓen rubuta sakamakon zaɓen.

Tun a daren jiya dambarwar ta fara a ɗakin tattara saakamakon zabe na helkwatar zaɓe ta ƙasa INEC reshen jihar Kano wanda jam”iyyar NNPP ta zargi cewar ba a gudanar da zaɓe ba kwata kwata illa hallaka mutane da aka yi a yankunan.

Ko aa yau maa sai da aka yi zargin wasu ƴan daaba da ƙone ofishin jam”iyyar NNPP a yankunan.

Ana zargin an ƙone mutane tara da ransu a cikin ofishin.

A ƙaramar hukumaar Takai ma akwai zargin ƙone ofishin zaɓe INEC na ƙaramar hukumar kuma ake zargin ba a gudanar da zaɓe ba a yankunan.

Sai dai hukumar zaɓe ba ta ce komai a dangane da hakan ba, amma ta tabbatar da cewar za ta bibiya tare da tabbatar da abin da ke faruwa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: