Bayan bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa a majalisar wakilai, dan gidan gwamnan kano Abba Abdullahi Umar Ganduje ya fadi zabe.

A jiya ne aka bayan sakamakon zaben na yan majalisun tarayya wadanda aka gudanar a ranar Asabar din data gabata.
A sanarwan da ta fito daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen Jihar kano ta bayyana Tijjani Jobe a matsayin wanda zai je majalissa na jamiyar NNPP.

Tijjani Jobe ya samu akalla kuri u 52,456 inda dan gidan Gwamnan kano Abba ya samu 44,808 a zaben.

Sannan hukumar zabe na ci gaba da bayyana yan majalisun tarayya wadanda ake ci gaba bayyanawa har zuwa yanzu.
A sakamakon hukumar zabe dai ta bayyana Barau I jibirin maliya a matsayin Dan majalisar datijai daga APC sai Kawu Sumaila daga jam’iyyar NNPP.
Sannan ko a jihar katsina jam’iyya mai mulki ta APC ta lashe dukkan kujerun sanataci uku.
Zamu ci gaba da kawo muku yadda take wakana a game da zaben Najeriya.