Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a ranar Asabar.

A yanzu haka shugaban hukumar zabe na kasa Mahmud Yakubu shi ne ya ke karabar sakamakon kowacce jiha yayin da baturen zabe ya kai babban birnin tarayyar Abuja.
Sai dai an bayyana sakamakon wasu daga cikin jihohin Najeriya.

Wasu daga cikin Jihohin da aka bayyana sune Jigawa katsina Legas Adamawa Gombe Ekiti Ondo dai sauaran jihohin da ake ci gaba da bayyanawa a ofishin hukumar zaɓe na jiha.

Sai dai a a dazu ne aka hango tsohon sanatan kogi ta Arewa Dino Malaye ya na yiwa shugaban hukumar zabe na kasa tsawa inda ya ke cewa ba za su yarda da zaben da aka yi a Ekiti ba.
Malaye ya ci gaba da cewa ba za su yarda da wannan sakamakon ba saboda a ciki akwai aringizon kuri u.
Duk da maganar da aka yiwa malaye ya bayyana cewa shi fa Dan kasa ne Kuma dan jamiyar PDP ne don haka yana da damar da zai yi magana.
Sai dai ana sa ran nan da Gobe Talata za a ayyana sabon shugaban kasan Najeriya ta bakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.