Yan sanda sun kama wani baturen zabe da ake zargi da yin magudi yayin tattara sakamakon zabe a jiya Lahadi a jihar Cross Rivers.

An kama baturen zaben mai suna MR Gabriel Agabi bisa tuhumarsa da laifin magudi yayin da yake irga kuri u lokacin lissafawa a babban ofishin hukumar zabe ta kasa INEC.

Cikin bayanin da aka bayyana ya nuna cewa Gobrial ya tare da wasu nambobi wadanda bai bayyana su ba ko kuma ma ya chanza su,

Sai dai an kama shi lokacin da aka duba babbar naurar yin zabe ta BVAS wadda ta bayyana gaskiya lamarin.

Sannan mutanen yankin hadi da wakilan jamiyyu sun bayyana cewa tun bayan kammala zabe a ranar Asabar da misalin karfe Shida an neme shi an rasa har zuwa karfe biyar na Asuba.

Yan sanda sun tisa keyar Wanda ake zargin zuwa ofishin hukumar su domin ci gaba da binceke.

Mr Gabriel Agabi Farfesa ne daga jami’an kalaba a jihar Cross Riva wanda yake a fannin falsafa Dan asalin Karamar hukumar Bakwarra a jihar.

Sai dai da aka tuntubi jin ta bakin kwamishinan yan sandan jihar Zannah shatima bai bayyana komai ba a kna lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: