Zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci hadin kan ƴan ƙasar domin yin aiki tare.

Tinubu wand atsohon gwamna jihar Legas ne ya bayyana haka a jawabin da ya yi bayan sanar da shi a matsayain wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Sannan ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin samar da cigaba a Najeriya.

Bola Tinubu wanda ya lashe zaben shugaban kasa karkashin jam”iyyar APC ya samu rinjayen ƙuri’u sama da miliyan takwas.

Sannan ya godewa miliyoyin mutanen da su ka zabeshi.

Sabon shugaban kasar Najeriya na biyar zai karɓi mulki daga hannun shugaba Buhari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: