Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC Abdusalam Abdulkarim Zaura a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano.

A na zargin Zaura da aikata laifuka da suka hada da zamba da damfara,
A Shari’ar wadda mai shari’a Muuhammad Nasir Yunusa ya jagoranta, an zargi A.A Zaura da cewa a wani lokaci a watan Ogusta, na shekarar 2014 ya karbi kudi kimanin dala dubu 200 daga Dr. Jamman Al-Azmi a jihar Kano, da nufin zamba da karya na wani kasuwancin hadin gwiwa.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa, bayan da lauyan mai gabatar da kara Aisha Tahar Habib ta karanta masa kunshin tuhumar.

Lauyan wanda ake zargi Ishaq Mudi Dikko SAN ya nemi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, a inda bayan ‘yar takaddama alkalin kotun Justiice Yunusa ya amince da bayar da belin.

Sai dai kotun ta dage cigaba da sauuraron shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Mayu na wannan shekara.
Za dai a fara shari’ar ne tun daga farko bayan da kotun daukaka kara ta soke saki da kuma wanke wanda ake zargin a kan laifin zamba da alkalin babbar kotun tarayya a Kano A.L Allagoa ya yi a baya.