Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri babban birnin jihar Borno domin wata ziyarar aiki ta kwana daya.

Shugaba Buhari ya isa birnin Maiduguri da misalin karfe 11 na safiya, a inda yake tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati.

Shugaban ya sami tarba daga gwamnan jihar Babagana Zulum da sauran tawagar gwamnatin jihar.

A na saran shugaba Buhari zai gana da ‘yan kasuwar da suka rasa shagunansu a wata gobara a babbar kasuwar jihar, da kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: