Akalla mutane goma ne ‘yan gida daya su ka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota da ya faru akan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachiya a lokacin da su ke dawowa daga wajen biki a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 5:00 na yamma a kusa da kauyen Makyerri inda su ka nufi garin Kachiya.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su maza ne ‘yan gida daya daga cikin su akwai masu Aure.

Rahotan ya ce motocim sun yi aran gama ne da wata motar dakon kaya da ke dauke da itatuwa wanda hakan ya hadda hadarin.

Wani mazaunin garin mai suna Isyaku Musa Kachiya ya shaiwa Daily Trust cewa wadanda su ka rasa rayukan su ‘yan asalin garin Kano ne amma su na zaune a garin na Kachiya da ke Jihar ta Kaduna.
Musa ya kara da cewa anyi jana’izar mutanen ne a yau Litinin kamar yadda addini ya ta nada.
Kwamanda a hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Jihar FRSC Zubairu Mato ya tabbatar da faruwar lamarin,inda ya ce daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu manya Takwas ne ya raya biyu.