Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta cire sunan dan majalisar Kano maai wakiltar Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa daga cikin wadanda suka lashe zaben bana.

A baya hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a jihar a zaben da aka yi ranar Asabar 25 ga watan Faburairu.

Baturen zabe na INEC, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai a baya ya ce, Doguwa na

APC ya ci zabe da kuri’u 39,732, inda ya lallasa abokin mahayyarsa na NNPP mai kuri’u 34,798.
Sai dai, a sabon jerin sunayen ‘yan majalisun da aka zaba, an nemi sunan Doguwa an rasa.
A cewar hukumar, an tilastawa baturen zaben na INEC ne a lokacin da ya ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben.
A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da baturen zaben ke karanta sakamakon zaben jikinsa na rawa.