Zababbun sanatoci 98 da ‘yan majalisun tarayya 325 ne su ka karbi takardun shaidar lashe zabe a bana a ofishin hukumar zabe ta INEC da ke Abuja.

 

A cewar rahoton jaridar The Nation, a yau Talata 7 ga watan Maris ne aka ba wadannan zababbun ‘yan siyasa takardun a hedkwatar INEC.

 

Sune ‘yan takarar da aka ayyana sun ci zaben da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun da ya wuce, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Idan baku manta ba, an yi zabe a Najeriya, inda aka sanar da Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa a Najeriya.

 

Sanatocin da aka zaba sun fito ne daga jam’iyyu bakwai na Najeriya da suka hada da APC, APGA, LP, NNPP, PDP, SDP da kuma YPP.

Jam’iyyar APC ta samu sanataoci 57, APGA 1, Labour 6, NNPP 2, PDP 29, SDP 2 da kuma YPP mai sanata 1.

 

A bangaren majalisar wakilai ta tarayya, jam’iyyar APC na da zababbun ‘yan majalisu 162, ADC 2, APGA 4, Labour 34, NNPP 18, PDP 102, SDP 2 sai kuma jam’iyyar YPP mai dan majalisa 1.

 

Da yawan ‘yan majalisun tarayyar da za su shiga majalisar a bana a matsayin sabbin zuwa, kamar yadda rahotanni su ka nuna.

A cewar rahoton, akwai tsaffin gwamnoni 11, tsohon mataimakin gwamna da kuma mataimakin gwamna mai ci a cikin zababbun sanatocin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: