An sake bude shagon sayar da kayayyaki na China a kasar Kenya mai suna China Square, bayan da ‘yan kasar ke nuna damuwa da yadda shagon mallakin ‘yan China ke sayar da kaya cikin rahusa.

Sai dai hakan ya jawo cece-kuce a fadin kasar a inda wasu ke ganin hakan wani saukine ga al’ummar kasar yayinda wasu ke ganin hakan zai karya ‘yan kasuwar kasar ne.

Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan manya da kananan ‘yan kasuwar kasar ne suka mamaye osishin mataimakin shugaban kasar a birnin Nairobi suna masu adawa da tsarin na ‘yan China tare da kira ga gwamnati da ta kawo karshen abin da suka kira Mamayar China a Kenya.

Bayanai daga Kenya sun tabbatar da cewa kwastomomi na yin tururuwa zuwa katin na ‘yan china wanda hakan ke fusata ‘yan kasuwar kasar.

Idan dai za’a iya tunawa ko a makon da ya gabata sai da aka rufe kantin na ‘yan China sakamakon wata zanga-zanga da ‘yan kasuwar Kenya suka gudanar sai dai a wannan lokacin ma al’ummar kasar na cigaba da nuna damuwaa tare da yin kira ga gwamnati da ta kawo karshen al’amarin cikin hanzari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: