Mataimakin gwamna kuma Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yayi alkawarin cewa, zai bawa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a gwamna.

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa dashi a Gidan Talabijin Na kasa NTA, cikin wani shiri mai taken “Tha Ballot”.

Gawunan yace “Karamar hukuma gwamnati ce mafi kusanci da al’umma, wajen abubuwan cigaba da rarraba ayyukan cigaban, a matsayina na tsohon shugaban karamar hukuma na san duk yadda al’amuranta su ke.”

“Lokacin da nake shugaban karamar hukuma an sakar mini dama nayi ayyuka, wannan yasa muka samu dumbin nasarori, idan aka zabe ni a matsayin gwamna zan dawo da wannan tsarin.” Gawunan ya fada.

Sannan yace shine Dan takara mafi cancanta na zama gwaman, sakamakon aiki da yayi tare da gwamnatocin baya ya samu gogewa da yawa, yayi alkawarin dora ayyukan cigaban da duk suka yi.

A karshe ya bukaci masu yin zabe da su guji tayar da husuma,su kama kansu suyi komai cikin zaman lafiya yayi gudanar da zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: