Wasu daga cikin gwamnoni sun soma shirye-shiryen shiga kotu da Ministan shari’a, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Jaridar Punch a yu Asabar ta rawaito cewa Gwamnonin za su yi karar AGF da kuma Gwamnan babban banki a kan zargin yi wa kotun koli rashin kunya.


Babban bankin Najeriya na CBN ya ki ba bankuna umarnin su yi biyayya ga hukuncin Alkalan kotun koli na cigaba da kashe tsofaffin N500 da N1000.
Sai a ranar Juma’a ne kotun koli ta gabatarwa gwamnatin tarayya da takardun shari’ar CTC na kotun koli, inda aka haramta soke tsofaffin kudin da aka yi.
Rashin samun takardun shari’ar ya hana tun farko gwamnatin tarayya ta ba Godwin Emefiele damar umartar bankuna su yi biyayya ga babban kotun kasar.
Lauyan Kaduna, Kogi da Zamfara a shari’ar da aka yi, Abdulhakeem Mustapha SAN ya sanar da cewa Abubakar Malami ya samu duk takardun shari’ar.
Daga yanzu Mustapha (SAN) ya ce za su san matakin da za su dauka idan AGF bai yi abin da ya dace ba.