Babbar kotun tarayya da ke zamanta a brinin tarayya Abuja ta bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC umarnin barin masu katunan zaben wucin -gadi da su kada kuri’a a lokacin zaben gwamnoni da ‘yan majalisar Jiha da za a gudanar a ranar 18 ga watan Maris din da mu ke ciki.

Alkalin Kotun mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da umarnin bayan da wasu mutane biyu su ka shigar da karar gaban kotun akan kotun ta baiwa hukumar ta INEC umarnin barin masu katunan wucin gadin su yi zaben.
Obiora ya bayyana cewa hukumar ta bar masu katunan su yi amfani da shi a lokacin zaben tunda an yiwa katunan rijista sannan bayannan su na cikin rijistar.

Alkalin ya kara da cewa wadanda su ka shigar da karar su na da ‘yancin yin amfani da katunan nasu na wucin gadi tunda bayanansu na cikin rijistar da su ka yi tare da sauran takardun zaben da hukumar da wallafa.

Obiora ya bayyana cewa umarnin da kotun ta bayar ya shafi iyakacin mutane biyun da su ka shigar da karar ne kawai ba tare da sauran masu zabe ba sakamakon wadanda su ka shigar da karar ba su shigar da ita da sunan wakilci ba.
Sannan Alkalin ya ce babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ko dokar zabe ta bayyana cewa iya kacin masu katunan zabe na dindindin ne kadai za su kada kuri’a.