Akalla mutane 9 ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a rukunin gidajen Grow Homes Estate da ke gefen Kuchibiyi, yankin Kubuwa a birnin tarayya Abuja.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ‘yan bindigan da suka kai adadin mutane 20 sun kutsa rukunin gidajen da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Jumu’a, suka aikata ɗanyen aikin.
Wani mazaunin Anguwar mai suna Hassan a takaice, ya ce maharan sun dauki mutane 9 a gidaje biyu da ke cikin rukunin Anguwar.

Mutumin ya kara da cewa harin ‘yan bindigan ya jefa mazauna yankin cikin yanayin fargaba da tashin hankali.

Ya ce da misalin karfe 11:30 wasu ‘yan bindiga da yawa suka kai hari rukunin gidajen Grow homes estate, kusa da Kuchibiyi.
Da aka tuntube ta, jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin, ta ce dakaru da masu gadin wurin sun mamaye dajin wurin don ceto mutanen.