Wasu ‘yan ta’adda sun hallaka wani yaro a lokacin da yake cikin gonar mahaifinsa a kauyen Ikefi da ke karamar hukumar Igalamela/Odulu ta Jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa batagarin sun hallaka matashin yaron ne a ranar Laraba bayan da ya sanar da mahaifin nasa wani na kokarin satar doya a gonar.
Wani Mazaunin kauyen Ajibili Achonu ya ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan yaron da mahaifinsa sun isa gonar, a lokacin ya bayar mahaifin nasa da nufin ya zagaya gonar.

Bayan tafiyar yaron zagaya gonar ya hango wani mutum na shirin kwashe musu doya, inda hakan ya sanya yaron ya tafi domin ya sanar da mahaifin nasa da ke wani bangare a cikin gonar.

Mazaunin garin ya kara da cewa a lokacin da yaron yake ihun barawo abokin tafiyar barawon da ke saman bishiya ya sauko tare da sanya makami ya hallaka yaron.
Bayan hallaka yaro an aike da gawarsa dakin ajiya gawarwaki da ke Ajaka hedkwatar hukumar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar SP William Aya ya bayyana cewa zai tuntubi baturen ‘yan sandan yankin domin samun cikakken bayani akan lamarin.